Canjin shugabancin Nijeriya | Siyasa | DW | 10.02.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Canjin shugabancin Nijeriya

Ana dai ci gaba da mayar da martani iri daban-daban dangane da naɗa mataimakin shugaban Nijeriya muƙamin shugaban riƙon ƙwarya sakamakon rashin lafiyar shugaba Alhaji Umaru Musa 'Yar Aduwa

Shugaban riƙon ƙwarya na Nijeriya Jonathan Goodluck

Shugaban riƙon ƙwarya na Nijeriya Jonathan Goodluck

A jiya ne dai majalisar dokokin Nijeriya ta tsayar da shawarar danƙa wa mataimakin shugaba Jonathan Goodluck al'amuran mulki na riƙon ƙwarya sakamakon rashin lafiyar shugaban ƙasa Alhaji Umaru 'Yar Aduwa...To ka yaya wannan manufar zata yi tasiri a manufofi na cikin gida da kuma dangantakar Nijeriya da ƙasashen ƙetare. Thomas Mösch ya tuntuɓi Dirk Kohnert, ƙwararren masani akan al'amuran Nijeriya a cibiyar nazarin manufofin Afirka ta GIGA dake birnin Hamburg inda ya fara da tambayarsa da cewar ko shin wannan ka iya zama mafita daga mawuyacin halin da Nijeriya ta samu kanta a cikin sakamakon rashin lafiyar shugaba 'Yar Aduwa, inda al'amuran kasar suka tsaya cik babu motsi?

"A haƙiƙa bana zaton haka, idan mun yi la'akari da manufofi na gajere da kuma dogon lokaci. Wannan shawara ce da aka daɗe ana sauraronta, musamman daga da yawa daga jami'an siyasar Nijeriya da na ƙasashen ƙetare. Abu ɗaya da za'a yi madalla da shi shi ne kasancewar a yanzu an shimma nasarar ɓarakar da aka yi shekaru gommai ana fama da ita game da al'amuran mulkin Nijeriya tsakanin arewaci da kudancin ƙasar, aƙalla a wannan halin da muke ciki yanzun, inda suka nuna hadin kai wajen naɗa mataimakin shugaban ƙasar a matsayin shugaban riƙon ƙwarya. To sai dai kuma ga alamu maganar zata kai gaban kotun ƙoli saboda ta saɓa da daftarin tsarin mulkin Nijeriya, wanda ya tanadi rubuta takarda da hannun shugaban ƙasa akan amincewarsa da miƙa mulki na wucin gadi ga mataimakinsa idan zarafi na rashin lafiya ya kama, lamarin da har yanzu bai faru ba, daga ɓangaren shugaba 'Yar Aduwa dake fama da rashin lafiya tun watan nuwamban da ya wuce yake kuma neman magani a ƙetare".

Tun dai a jiya aka fara samun wasu dake nuna cewar wannan shawara da majalisun dokoki da dattawan Nijeriya suka ɗauka zai ƙara tsaurara halin da ake ciki, musamman saboda kasancewar zai haifar da cece-ku-ce game da daftarin tsarin mulkin Nijeriya. To ko hakan na ma'ana ne cewar a cikin kwanaki masu zuwa za a fuskanci ƙarin rikici ne kamar yadda aka saba a Nijeriyar?

"A'A a ganina hakan ba zai haifar da wani rikici ba, saboda wannan magana ce da ta shafi tsarin doka, amma su kansu jami'an siyasa dake da faɗa a ji, kamar yadda na faɗa tun farko, suna goyan bayan wannan mataki na danƙa wa mataimakin shugaban madafun iko saboda kamar yadda na faɗa tun farko, al'amura sun tsaya cik kuma wajibi ne a fara farfaɗo da su, misali harkar kasuwancin man da Allah Ya fuwace wa Nijeriya, wanda wasu tsiraru 'yan gata ke cin gajiyarsa. Ka ga su ne zasu yi asara idan ƙoƙarin sasantawar da shugaba 'Yar Aduwa ya gabatar ya ci tura. Domin kuwa a sakamakon rashin lafiyar shugaban na Nijeriya an dakatar da shawarwarin samar da zaman lafiyar ita kuma ƙungiyar MEND da sauran ƙungiyoyi na yankin sun fito fili sun nuna cewar har yau a shirye suke su kawo cikas ga ayyukan haƙan man a Niger Delta."

To shi kansa Jonathan Goodluck dai ɗan Nigerdelta ne, kuma wannan shi ne karo na farko da wani jami'in siyasa daga wannan yanki ya kama wani babban muƙami na matsayin mataimakin shugaban ƙasa, a yau kuma ya wayi gari a matsayin shugaban ƙasa, ko shin yana da ikon taka rawar gani a shawarwarin sasantawar, kamar yadda ya nunar a jawabinsa cewar zai ci gaba da wannan manufa ta shugaba 'Yar Aduwa?

"A ganina ba shakka game da haka, kasancewar, kamar yadda ka ce, ya fito ne daga wannan yanki kuma har yau a Nijeriy abin takaici, ƙabilanci na taka muhimmiyar rawa a al'amuran yau da kullum. A saboda haka kasancewar shugaban na riƙon ƙwarya ya fito ne daga yankin kudu-maso-gabacin Nijeriya, hakan ka iya zama alheri ga makomar shawarwarin sulhu."

To idan mun koma matsayi dangantakar ƙasa da ƙasa, inda ba shakka aka riƙa yi wa 'yan siyasar Nijeriya matsin lamba domin tinkarar mawuyacin halin da ake ciki, to ko shin kafofi na ƙasa da ƙasa a yanzu sun gamsu da abin da ya faru a Abuja a jiya talata?

"Ko shakka babu, musamman ma Amirka, wadda ta damu matuƙa ainun sakamakon harin ta'addanci na baya-bayan nan, wanda wani ɗan Nijeriya da ya fito daga wani gida mai wadata da martaba a Nijeriyar ke da alhakinsa. Wannan ya sanya siyasar duniya da zura ido kan Nijeriya dangane da manufar murƙushe ta'addanci a duniya. Hatta a kwamitin manufofin ƙetare na majalisar dokokin Jamus, sai da aka bayyana min baya-bayan nan cewar a halin yanzu an damu da maganar Nijeriya saboda hali na ɗarɗar da ƙasar ke fama da shi."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu