1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cameron zai yi jawabi bisa makomar Birtaniya cikin EU

Usman ShehuJanuary 23, 2013

Ana saran Firayim ministan Biratiya David Cameron zai yi jawabi, inda a ciki zai nemi 'yan ƙasar su yi ƙuri'ar jin ra'ayi, a kan ko akwai buƙatar ficewar ƙasar a ƙungiyar EU

https://p.dw.com/p/17Q0C
Britain's Prime Minister David Cameron delivers his keynote speech at the Conservative Party conference in Birmingham, central England October 10, 2012. REUTERS/Darren Staples (BRITAIN - Tags: POLITICS)
David Cameron, Firayim ministan BirtaniyaHoto: Reuters

A yau ne firayim ministan Birtaniya David Cameron zai yi jawabi ga kungiyar Tarayyar Turai, wanda a ciki ake saran cewa zai bayannar da makomar kasarsa a kungiyar Tarayyar Turai, idan ya sake lashe zaben da zai gudana a shekarar 2015. Wata sanarwa da aka bayar a birnin London ta nunar da cewa, Cameron zai shiga tattaunawa tare da sauran kasashen Turai game da zaman kasarsa mamba ta kungiyar TarayyarTurai kafin daga bisani a gudanar da zaben raba gardama. Cameron yace al'umumar Birtaniya sun kai matuka a fushinsu game da take-taken kungiyar Tarayyar Turai . Su dai masu nuna shakkunsu da kungiyar sai kara samun karfi suke yi a jam'iyyar firimiyan. Gwamnain Birtaniya ta dade tana son ganin ta shiga sabuwar tattaunawa akan yarjejeniyar kungiyar Tarayyar Turai, musamman game da aikin sharia. Su dai abokan aikin Birtaniya na ƙungiyar Tarayar Turai za su ci gaba da yin sukan wannan matsayi.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Usman Shehu Usman