Cafke wadanda suka kashe Al-bani | Labarai | DW | 03.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cafke wadanda suka kashe Al-bani

Hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya wato SSS, ta gabatar da mutane bakwai da suka amsa cewa sune su ka kashe wani fitaccen Malamin addinin Musulunci a kasar.

A ranar 21 ga watan Fabarairun da ya gabata ne dai aka kashe fitaccen malamin addinin Islaman da ke garin Zariya a jihar Kadunan Najeriya Sheikh Auwal Adam Albani da dansa da kuma matarsa a birnin na Zazzau, bayan da ya taso daga karatun da ya kan yi da daddare

Jami'ar yada labarai ta hukumar ta SSS Merlyn Ogar ce ta gabatar da mutanen guda bakwai da suka amsa cewa su 'ya'yan kungiyar nan ta Boko Haram ne ga manema labarai. Mutanen sun hadar da Yakubu Abdullahi da Ibrahim Shu'aibu da ake kira da Abu Ammar da Musa Abubakar da kuma Yasir Ibrahim Salihu. Daya daga cikin mutanen da ake tuhuma Bilyaminu Usman ya bayyana tabbatar da cewa sune suka kashe marigayi Sheikh Auwal Albani.

Wakilinmu na Abuja Uwais Abubakar Idris ya ruwaito cewa mutanen da suka ce su 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne, sun bayyana cewa sun kashe malamin ne saboda koyarwasa ta sabawa akidarsu kuma sun kitsa yadda suka kai harin da ya yi sanadiyar hallaka shi da matasarsa da kuma dansa a unguwar Hayin Danmani da ke Rigasa a jihar Kadunan.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Editor: Mohamaduo Awal Balarabe/LMJ `