Côte d′Ivoire: Ouattara zai sha kaye in ji abokan hamayya | Siyasa | DW | 10.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Côte d'Ivoire: Ouattara zai sha kaye in ji abokan hamayya

'Yan takaran da za su kalubalanci shugaba mai ci Alassane Ouattara sun sha alwashin yin hakan ne bayan da kotu ta amince da takararsa.

Wannan ya biyo bayan amincewar da kotu ta yi da Ouattara a matsayin dan takara duk da zargin da ake yi masa cewar shi ba cikakken dan kasa ba ne. 'Yan takara goma ciki har da Alassane Ouattara ne kotun tsarin mulkin Côte d' Ivoire ta amince su tsaya a zaben shugaban kasa da ke tafe. Sai dai kuma tun ba a je ko'ina ba wasu daga cikinsu sun fara kiran magoya bayansu da su tayar da kayar baya, saboda nuna cewar shi shugaban na Côte d 'ivoire mai ci a yanzu ba dan asalin kasar ba ne.

Sun dogare ne kan wani sashe na kundin tsarin mulki da ke cewar sai wanda iyaye da kankaninsa da ke da tsatso da kasar ne ke da 'yancin tsayawa takara. Alhali kakannin Ouattara sun fito ne daga Burkina Faso.

Saboda haka ne jam'iyyar FPI ta tsohon shugaba Gbagbo ta ce dan takararta zai kaurace wa zaben matikar Ouattara bai janye ba. Yayin da gamayyar jam'iyyun adawa ta CNC ta ce za su gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da duk mataki na amincewa da Alassane Ouattara a matsayin dan takara. A cewar Brice Delagneau da ke zama shugaban wata kungiya mai zaman kanta a côte d' Ivoire, shure-shuren kaiwa gaci da 'yan takara ke yi ba ya rasa nasaba da sharhunan da jaridun kasar ke yi a kan zaben na shugaban kasa.

Mai yiwuwa Outtara ya kai labari in ji manazarta

Manazarta harkokin siyasa sun yi ammanar cewar Alassane Ouattara ne zai iya kai labari a zaben shugaban kasa na 25 ga watan Oktoba saboda kawunann sauran 'yan takaran tara na rabe. Sannan kuma baya ga bunkasa tattalin arzikin kasarsa da ya yi a wa'adin mulkinsa na farko, shugaban na Côte d' Ivoire ya na kokarin dinke barakar da ta kunno kai bayan rikicin da ya biyo bayan zaben na 2011. Idan za a iya tunawa dai fiye da mutane dubu uku ne suka rasa raqyukansu a tashin hankalin da ya biyo bayan kin amincewar da shan kaye da tsohin shugaban Laurent Gbagbo ya yi.

Tuni ma wasu 'yan Côte d' Ivoire suka fara tunanin bari kasar kafin ma a gudanar da zaben domin kada wani sabon rikici ya barke kuma ya ritsa da su. Mininstan cikin gidan Côte d' Ivoire Hamed Bakayoyko ya gargadi duk 'yan siyasa da su guji haddasa rigima a zaben shugaban kasa da ke tafe idan suna son kansu da lafiya. Kotun tsarin mulkin wannan kasa ta yi tankade da rairaya daga cikin 'yan takara 33 kafin daga bisani ta amince da takardun mutaqne 10.

Sauti da bidiyo akan labarin