Côte d′Ivoire da sojoji sun cimma matsaya | Labarai | DW | 14.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Côte d'Ivoire da sojoji sun cimma matsaya

Gwamnatin Côte d 'ivoire ta amince da biyan sojoji masu bore rabin kudin da suka bukata na albashi da alawus bayan da suka shafe sa'o'i na tattaunawa a birnin Bouake.

Gwamnatin Côte d' Ivoire ta cimma yarjejeniya da sojojin kasar da ke bore kan batun biyansu albashi da kuma alawus, bayan da bangarorin biyu suka shafe sa'o'i suna tattaunawa tsakaninsu. Wannan dai shi ne karo na biyu da ministan tsaron kasar Alain-Richard Donwahi da kuma sojoji suka cimma matsaya kan wannan batu a cikin mako guda.

Sojojin wadanda daga cikinsu akwai tsofoffin 'yan tawaye sun nemi gwamnati ta biyasu miliyan goma na CFA  a matsayin albashi da alawus da suke binta. Sai dai bisa ga yarjejeniyar da suka cimma kowani soja daya zai samu rabin abin da ya bukata tun da farko wato miliyan biyar na CFA.

Sai dai sojoji sun kewaye birnin Bouake a lokacin tattaunawar tare da yin harbe-harben bindiga a wasu birane da ke sassan kasar domin nuna fushinsu. Ita dai gwamnatin Côte d' Ivoire tana neman warware boren sojojin Bouake cikin ruwan sanyi sakamakon kaurin suna da birnin ya yi wajen tayar da zaune tsaye lokacin rikicin siyasa na shekarun baya.