Burunai: Dakatar da kisa ga 'yan luwadi
May 6, 2019Majalisar Dinkin Duniya dai ta bayyana dokar da aka nemi ta fara aiki a ranar uku ga watan Afrilu da zama mai tsaurin da ya wuce kima, yayin da Amirka da sauran wasu kasashe suka nemi Burunai ta dakatar da wannan shiri na jefe 'yan luwadi da mazinatan. Fitattun mutane da suka hadar da George Clooney da Elton John da sauransu sun yi kira na a kaurace wa otel-otel tara a Amirka da nahiyar Turai da ke da alaka da Burunai.
A jawabin da ya yi a ranar Lahadi gabanin fara watan Azumin Ramadana Sultan Hassanal Bolkiah ya bayyana cewa yana sane da tari na tambayoyi da rashin fahimta karkashin dokar ta Shari'a amma ya ce babu wani abu na haifar da fargaba.
A martani da ta mayar a wannan Litinin kan batun, babbar sakatariyar kungiyar Commonwealth Patricia Scotland ta ce dakatar da dokar kisan abun yabawa ne haka kuma akwai bukatar Burunai ta janye dokoki da suka hadar da yanke hannun masu laifin sata da ma yin bulala.