1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Burtaniya: Alhinin kamuwa da cutar daji da Kate ta yi

March 23, 2024

Gimbiyar Wales ta masarautar Burtaniya Kate Williams ta sha jinjina da kauna daga ciki da wajen kasar bayan an sanar da cewa tana dauke da cutar daji makonni da sanar da cewa Sarki Charles na dauke da makamanciyar cutar.

https://p.dw.com/p/4e39H
Gimbiyar Wales ta Masarautar Burtaniya, Catherine a yayin da ta wallafa bidiyon halin da ta ke ciki na lalurar cutar daji.
Gimbiyar Wales ta Masarautar Burtaniya, Catherine a yayin da ta wallafa bidiyon halin da ta ke ciki na lalurar cutar daji.Hoto: BBC Studios/Avalon/Photoshot/picture alliance

Sanarwar da aka fitar ya sanya shakku da kuma damuwa kan yadda manyan masu rike da sarautar Burtaniya ke fama da cutar daji. Watanni 17 da hawa kan gadon sarautar Burtaniya, fadar Burkingham ta sanar da cewa Sarki Charles III na dauke da cutar daji wanda hakan ya sanya soke dukkan wasu muhimman  ayyukan da Sarkin ke gudanarwa.

Karin bayani: Auren Yarima William

Jaridun Burtaniya sun rawaito Firaiministan kasar Rishi Sunak da fadar White House na Amurka sun yi jinjina ga gimbiya Kate juriyar da ta nuna kamar yadda kalaman su suka mamaye shafukan jaridun Burtaniya dauke da hoton Gimbiya Kate.

Karin bayani: Sarki Charles III ya yi alkawarin koyi da mahaifiyarsa

A jawabin da ta wallafa a shafinta na X Gimbiya Kate ta ce ta kadu matuka bayan likitoci sun sanar da ita cewa tana dauke da cutar Cancer, bayan an dauki tsawon lokaci ana gudanar da bincike.