Bunkasar tattalin arzikin Libya | Siyasa | DW | 29.04.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bunkasar tattalin arzikin Libya

Gwamnatin Libya ta ce zata bulo da matakai na farfado da tattalin arzikin kasa

Shugaban Libya Moummar Gaddafi

Shugaban Libya Moummar Gaddafi

A yayin da kasar Libya mai yawan aluma miliyan biyar da dubu dari biyar ke cigaba da kokarin samar da manufofi na farfado da tattalin arziki kasa,gwamnan baban bankin kasar ta Libya Ahmed Menesi cikin hirar da yayi da kamfanin dilancin labaria na Reuters yayi da shi,ya baiyana cewa gwamnati zata dauki matakai na sayar da jarin kamfanonita ga masu hanu da shuni na kasar,saboda yin hakan zai taimaka wajen samar da aiyukan yi ga alumar kasar bayan da gwamnati ta salami maikatan dake aiki a kamfanoninta.

An dai baiyana cewa gwamnatin shugaba Kadafi na Libya ta sami sukunin bulo da sabin matakai na farfado da tattalin arziki ne,bayan da Amurka ta cirewa Libya takunkumin tattalin arziki data kakaba mata a sabili da matakan data dauka cikin watan Disamban da ya gabata na lalata shirinta na kera makamai na nukiliya.

Matakan dai da gwamnatin Libya ta dauka na sayar da jarin kanana da kuma manyan kamfanoninta da suka tasama 360,zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin kasar,to sai dai kuma da dama daga cikin yan asalin kasar ta Libya kamar wani mutum mai suna Khaled bai sami kafar samu aiki a fuskar gwamnati ba,yayin da wadanda ma suke aiki a gwamnatin ma tilas sai sun hada da wani aikin kafin su sami abinda zasu iya ciyar da iyalan su.

Dan asalin kasar dai ta Libya Mohammed Khalid mai shekaru 23 da haihuwa mai sana’ar tukin Taxi,ya baiyana cewa ya gwamaci yayi sana’arsa ta tukin Taxi mai makon aikin gwamnati,saboda a duk lokacin da yayi dauki fassinja daya a nisan zango yana samun dinar 15 kimanin dolar Amurka 11.

Yawanci dai gwamnatin Libya na biyan maikata alabshin dola 200 mafi karanci a duk wata na Allah,lamarin kuma masana tattalin arziki suna nuna cewa yayi kadan ta la’akari da tsadar da ake fuskanta ta rayuwa a kasar ta Libya,yayin kuma duk da haka maikata da dama a koda yaushe ke asarar aiyukan su a maikatun gwamnati.

Jami’an diplomaciya na kasahen duniya,sun yi nuni da cewa baban kalubalen dake gaban gwamnatin kasar Libya shine magance matsaloli na rashin aikin yi da a koda yaushe ke kara ta’azara a tsakanin alumar wanan kasa ta arewacin Africa.

Kasar dai ta Libya dake zaman memba a kungiyar kasahe masu arzikin mai na duniya ta OPEC a takaici,nada rarar ajiyar danyan mai da ya kai ganga biliyan 36,wanda kuma aka baiyana da cewa zata iya rubanya yawan wanan adadi da take da shi,don samar mata da karin kudaden shiga na kasa matukar dai zata kara bunkasa harkokinta na hako mai.

Jami’an dilomaciya na yammacin Turia sun yi nuni da cewa tattalin arzikin Libya zai iya bunkasa,matukar dai gwamnati a birnin Tripli zata karkata alakar irin kudaden da take kashewa wajen shirinta na kera makamai na nukiliya wajen bulo da managartan matakan da zasu taimaka wajen farfado da tattalin arzikinta.

A nasa bangaren shugaban gungun kamfanonin zuba jari na Libya,Rajab Shalgabu,ya shaidawa mahalarta baban taron harkokin kasuwaci su kimanin 400,cewa gwamnatin Libya zata bulo da sabin matakan da zasu janwo hankalin masu zuba jari na ketare su zuba jarin su a a wanan kasa ta arewacin Africa.

Jamilu Sani.