Bullar cutar murar tsuntsaye a Beijing | Labarai | DW | 13.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bullar cutar murar tsuntsaye a Beijing

Wata yarinya mai shekaru bakwai da haihuwa ta harbu na nau'in H7N9 na murar tsuntsaye a babban birnin China.Ya zuwa yanzu dai mutane 11 cutar ta kashe a kasar ta China.

Sabon nau'in cutar murar tsuntsaye na H7N9 ya fara yaduwa zuwa wasu sassa na kasar China. Hukumomin kiwon lafiyar a babban birnin kasar wato Beijing sun nunar a wannan asabar cewar wata yarinya mai shekaru bakwai da haihuwa ta harbu da kwayar cutar ta murar tsuntsayen. Ya zuwa yanzu dai an hakikance cewar mutane 43 dukkaninsu a gabashin China ne suka kamu da wannan nau'in cutar, inda 11 daga cikinsu suka riga suka bakwanci lahira.

Hukumar lafiya ta duniya wato WHO ko kuma OMS ba ta kai ga sanyata a matsayin wata annoba da ya kamata a kawar cikin gaggawa ba, saboda cutar ta bazu ne kawai a Shanghai da kuma wasu larduna da ke makobtaka da ita. Har yanzu kwararru ba su tabbatar ko kwayar cutar H7N9 na yaduwa daga mutum zuwa mutum ba. Ita ma dai hukumar zartaswa ta Kungiyar Gamayyar Turai ta nunar da cewa babu wani dalili da zai sa 'yan kasashen Turaisu nuna fargaba game da wanan cuta.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mouhamadou Awal