Bukukuwan Sallah a cikin fargaba a Najeriya | Siyasa | DW | 28.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bukukuwan Sallah a cikin fargaba a Najeriya

Yayin da bukukuwan Sallah suka gudana cikin kwanciyar hankali a Nijar, a Najeriya lamarin ba haka yake ba sakamakon hare-haren da aka kai a Kano.

Mutane guda uku ne suka rasa rayukansu kana wasu kuma da dama suka jikkata,a lokacin da wata yar ƙunar baƙin wake ta kai harin bam a babban kamfanin kula da harkar man fetir na NNPC da ke a unguwar Hotoro a birnin Kano.

Bam ɗin ya fashe a sa'ilin cinkoso jama'a a bakin NNPC

Shedun gani da ido sun bayyana cewar wata mata ce ta zo da bam ɗin ɓoye a cikin kayanta ta kuma kutsa inda jama'a da dama suka yi layi domin sayen kalanzir a kamfanin. Sakamakon kamawa da wuta da injin wannan kamfanin ya yi mutane da dama sun ƙone. Matar da ta kai harin dai tana sanye ne da Hijjabi, lamarin da ke nuni da cewar maharan sun fito da sabuwar hanyar yin amfani da mata wajen kai hare-haren.

A Nijar bikin Sallah ya gudana lami lafiya

Ɗaukacin al'ummar Nijar sun gudanar da bukukuwan na Sallah ne a yau a kusan dukkanin cikin jihohin ƙasar. A Damagaram dubban jama'ar ne suka yi adduo'i na samar da zaman lafiya a ƙasar saboda tashe-tashen hankula da ake fama da su na rashin tsaro a yankin Sahel da kuma maƙobciyar ƙasar wato Najeriya.

Daga ƙasa za a iya sauraron rahoton da wakilinmu na Kano Nasir Salisu Zango ya aiko mana, haɗe da rahotannin da wakilanmu na Zinder da Ghana da kuma Masar suka aiko mana dangane da bukukuwan na Sallah

Mawalafi : Nasir Salisu Zango
Edita : Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin