1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukukuwan sabuwar shekarar 2019 a duniya

Abdullahi Tanko Bala
December 31, 2018

Kasashen duniya na murnar shiga sabuwar shekarar 2019 tare da wayan wuta da kuma kyakkyawar fata ta wanzuwar zaman lafiya hadin kai da cigaban tattalin arziki a duniya baki daya.

https://p.dw.com/p/3ApVw
Neujahr 2019 | Sydney, Australien
Hoto: Getty Images/B. Hemmings

Jama'a a fadin duniya a yau litinin suna bankwana da shekarar 2018 da aka fuskanci kalubale wadanda suka hada da kasuwanci da siyasa da kuma addini a yawancin kasashe.

Yankin Kiribati na tsibirin Pacific shine na farko a duniya da ya shiga sabuwar shekarar 2019, yankin da ya sha fama da matsalolin sauyin yanayi a 2018.

A birnin Auckland na kasar Newzealand kuwa dubban jama'a ne suka yi dandazo domin kallon wasan wuta ta yin maraba da sabuwar shekarar 2019.

A sakonsa na sabuwar shekara, sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ja hankali da taka-tsantsan kan matsalolin sauyin yanayi, yana mai cewa wannan ne lokacin da ya kamata a hada hannu domin magance matsalar da kare kimar dan Adam da kuma kyautata makoma mai kyau a gaba.

A nata jawabin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi tsokaci da cewa 

"Daga ranar 1 ga watan Janeru Jamus za ta zama mamba a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya na shekaru biyu, inda za ta yi amfani da wannan dama wajen kokarin warware matsalolin da suka addabi duniya. Za mu kara yawan kudi domin taimakon jinkai da gudunmawar raya kasa da kuma tsaro. Muna da kudiri mai karfi na tabbatar da hadin kan tarayyar Turai. Muna kuma fatan karfafa kawance da Birtaniya bayan ficewarta daga kungiyar tarayyar Turai".