Bukukuwan Ista cikin fargaba a wasu sassan Najeriya | Siyasa | DW | 29.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bukukuwan Ista cikin fargaba a wasu sassan Najeriya

Yayin da mabiya addinin Kirista a duniya ke gudanar da bukukuwan, tabarbarewar tsaro a arewacin Najeriya sun hana yin bikin Istar kamar yadda aka saba.

Tabarbarewar lamuran tsaro dai musamman a yankin arewa maso gabashin tarayyar Najeriya inda aka fi samun hare-haren bama-bamai da bindigogi ya durkusar da harkokin rayuwar al'umma dabam-dabam.

Rahotanni na nuna cewa wannan matsalar ta haifar da samun koma baya ga masu zuwa majami'u inda yanzu haka Kiristoci da dama ke kaurace wa zuwa Coci kamar yadda suka saba yi a baya saboda hare-hare da aka kai wa wasu majami'u a baya.

Bukukuwan da Kiristoci ke yi a lokuta dabam-dabam kamar Kirsimeti ko Ista na daga cikin harkokin da suka samu koma baya ko dai saboda fargabar abin da ka iya faruwa ga masu yin bukukuwan ko kuma gargadi da ake samu wani lokaci daga jami'an tsaro na yiwuwar kai hari a irin wannan lokaci.

Fargabar kai hare hare lokacin Ista

Wannan shi ne yanayin da ake ciki a yankin arewa maso gabashin Najeriya da ma wasu sassa na arewacin kasar, inda shirin gudanar da bukuwan Istar ke fuskantar barazana saboda yadda hare-hare suka tsananta a wannan yanki duk da cewa dai ya zuwa yanzu babu wata sanarwa daga jami'an tsaro dake nuna cewa za'a kai hare-hare a irin wannan lokaci.

Generalvikar Peter Ebidero steht am 10.03.2007 vor der katholischen Kirche in Kano im mehrheitlich muslimischen Norden Nigerias. Anders als im Süden gilt hier die islamische Rechtssprechung, die Scharia. Christen haben es hier sehr schwer, die Universität zu besuchen oder eine Arbeit zu finden. Foto: Ulrike Koltermann (zu dpa-Reportage: Halleluja-Hysterie und Scharia in der religiösesten Nation der Welt vom 21.03.2007) +++(c) dpa - Report+++

Peter Ebidero, babban mai kula da majami'ar Katholika a Kano

Evangelist Musa Misal shugaban matasa na kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen arewa maso gabashin Najeriya ya yi karin haske kan irin fargabar da Kiristoci ke ciki dangane da bukuwan Ista da suka yi a daga ranar Juma'a zuwa Litinin.

"Dab da ista abubuwa da dama sun yi ta faruwa da a da aka yi tsammanin cewa an samu kwanciyar hankali. Wurare kamar su Maiduguri, Yobe, Kano, inda wasu Kiristocin ma ke barin gari. Wasu ma ba sa iya zuwa wuraren ibada."

A wasu jihohin yankin dai ana shirin yin kwarya-kwaryar bukukuwan cikin tsauraran matakan tsaro inda wasu jihohin kuma ma da wuya a yi wannan bukukwa saboda tsoron abin da ka iya faruwa.

Gudanar da Ista a gida maimakon a coci

Mafi yawan masu gudanar da wannan bukukuwan dai musamman a jihohin Borno da Yobe sun bayyana cewa sun zabi su yi bukin a gidajen su ba tare da halatar majami'u ba saboda fargabar da suke ciki.

Anschläge auf Kirchen in Nigeria Afrika ARCHIV

Coci da yawa sun kasance wayam yayin Ista a arewacin Najeriya

Sai dai Shugabannin mabiya addinin kirista na wannan yankin na ba su kwarin guiwar fitowa don yin bukin kamar yadda aka saba saboda: "imani da suka yi da cewa mutuwa in ta zo tana iya samun mutum a duk inda yake", inji Rev. Abari Kalla shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Gombe.

To sai dai jami'an tsaro a nasu bangaren sun bukaci mutane su kwantar da hankulan su kuma su ci gaba da shirin bukin tare da ba da tabbacin cewa za su yi bakin kokarin su na ganin sun murkuhe duk wani shiri na kai hari ga masu gudanar da bukukuwan.

Mawallafi: Alamin Suleiman Mohammed
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin