1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar mutunta juna ta fito a taron Commonwealth

June 24, 2022

Shugabannin kasashen da ke halartar taron kasashe rainon Ingila a Ruwanda, sun bukaci da a mutunta juna da ganin kowacce kasa a matsayin 'yantatta.

https://p.dw.com/p/4DD7A
Ruanda Kigali |  2022 Commonwealth Heads Of Government Meeting
Hoto: Luke Dray/Getty Images

Manyan-manyan batutuwan da suka dauki hankali a wurin taron sun hada da yadda za a magance matsalar sauyin yanayi da wasu cututtuka da suka addabi kasashen, har ma da yadda shugabannin kasashen za su tayar da komadar tattalin arzikin kasashensu bayan cutar corona.

Shugabannin da ke halartar taron a birnin Kigali na Ruwanda sun hada da firaministan Canada Justin Trudeau da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da firaministan Birtaniya Boris Johnson da sauran shugabanni. Sai dai kuma hankalin taron ya yi saurin bitar yadda rikicin Ukraine ke haifar da koma-baya a tsakanin mambobi. Firaminitsan Burtaniya ya yi bayani yana mai cewa.

''Daya daga cikin manyan abubuwan da muke adawa da su a wannan kungiya, shi ne mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine da kuma toshe tashoshin jiragen ruwa da ake wucewa da abinci zuwa ga mutanen duniya da ke fama da talauci. A yanzu haka kusan ton miliyan 25 na masara da alkama na nan Rasha ta hana a fitar da shi daga Ukraine.''

Boris Johnson UK und  Paul Kagame Ruanda
Hoto: Eddie Mulholland/ASSOCIATED PRESS/picture alliance

A gabanin taron dai kungiyar ta Commonwealth ta sanya kasashe daukar alkawarin tara sama da Dala biliyan hudu domin yaki da cutar Maleriya da wasu cututtuka a kasashen kungiyar. Taron wanda Shugaba Paul Kagame na Ruwanda ya bude shi ya ba kasashen Commonwealth damar tsara abubuwan da za su gabatar a yayin babban taron duniya a kan sauyin yanayi da za a yi a watan Nuwamba mai zuwa a kasar Masar. Patricia Scotland ita ce sakatare janar na kungiyar ta Commonwealth.

''Barnar da zuwan corona ya yi mana da basussukan da ke kanmu na ci mana tuwo a kwarya. Ci gaba da tabarbarewa ta sauyin yanayi na yin barazana a gare mu; ga kuma rikici da rashin zaman lafiya kusan ko'ina a wannan duniya. Tashin farashin abinci da fetur, su ma na haifar da barazana. Wannan taro namu dama ce  ta mu samar da amsoshi ga wadannan tambayoyi.''

Sarauniya Elizabeth ta Ingila ce dai ke jagorantar kungiyar, sai dai a wannan karon ta aiko danta, Yarima Charles ya wakilce ta. To amma duk da haka kasashen da ke adawa da tsoma bakin gidan sarautar Birtaniya a cikin kungiyar, sun nuna bacin ransu a kan yunkurin da ake yi na tabbatar wa da Yarima Charles ragamar kungiyar a kaikaice. 

Kasashen da ke cikin wannan kungiya ta Commonwealth dai sun kunshi kusan duk wata kasa da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka su 54. Sai dai ana sa ran a yayin taron shugabannin kasashen kungiyar za su amince da kasashen Togo da Gabon a matsayin mambobin kungiyar, duk da cewa ba Birtaniya ba ce ta raine su.