1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buƙatar wadata al'umma da ingantaccen ruwa

February 21, 2013

Yunƙurin mika wa kamfanoni masu zaman kansu, harkokin samar da ruwan sha ga al'umma na fuskantar matsaloli a sassa daban daban na duniya.

https://p.dw.com/p/17ijH
Hoto: picture alliance / Photoshot

Alhakin samar da isasshen ruwan sha mai tsabta a nan Jamus, bisa al'ada, abu ne da dake hannun ƙananan hukumomi. Waɗannan gundumomi ne suke da nauyin shimfiɗa bututun kai ruwan zuwa duk inda ake bukatarsa da sanya isassun fanfunan da ake bukata a duk inda ake bukatarsu. Lokaci-lokaci kananan hukumomi ko gundumomin sukan mika kwantaragin tafiyarda wnanan aiki ga kamfanoni masu zaman kansu domin tabbatarda isasshen ruwan ya samu ga kowa da kowa. Duk da haka, ba'a cika samun inda fannin samar da ruwa ake mika shi gaba daya ga irin wadannan kamfanoni masu zaman kansu ba. Umaru Aliyu yana dauke da karin bayani.

A nan nahiyar Turai yanzu dai an fara nazari game da daidaita al'amuran da suka shafi hidimomin yau da kullum ga jama'a, abin da ya hada har da samar da ruwa. Hukumar kungiyar hadin kan Turai tun a karshen shekara ta 2011 ta gabatar da tsarin na daidaita aiyukan jin dadin jama'a yadda zasu zama bai-daya a nahiyar Turai, inda ake sa ran majalisar Turai dake Strassbourg zata yi muhawara, ta yanke kudiri a game da wannan tsari na doka. Duk da haka, kananan hukumomi da gundumomi, musmaman a nan Jamus suna adawa da wnanan shiri na kungiyar hadin kan Turai, saboda tsoron idan har aka gabatar dashi, hakan zai sanya su rasa ikon su na kula da al'umarsu kai tsaye. Suna kuma ci gaba da nunar da cewar batun samar da ruwa, al'amari ne da akan daidaita shi da bukatunwurin da za'a bada ruwan, ato a takaice, ko wane yanki dabam yake a fannion bayar da ruwan. Hans Joachim Reck, shugaban kungiya ta kula da aiyukan kananan hukumomi yace batun samar da karfin lantarki ana iya daidaita shi ya zama bai-daya a Turai amma yin haka a fannin ruwa ba zai yiwu ba.

Rural water pump near Ulundi.South Africa
Hoto: CC/World Bank Photo Collection

Matsalar samar da ruwa ga jama'a shine rashin kiyaye tsabtan ruwan, ko rashin kiyaye sharuddan kula da hanyoyin samjar da ruwan, abin da a karshe zai zama mai hadari samar da ruwan mai tsabta. A duk inda aka kyale batun samar da ruwa ga jama'a a hanun kamfanoni masu zaman kansu, misali a Ingila ko a Faransa, jam'a sun ga mummunan sakamakon da hakan ya haifar. Wannan ma shi ya sanya a karshe batun samar da ruwan a birnin Paris ya sake komawa a hannun gundumar birnin.

Shima Mathias Ladstätter, masani kan harkokin ruwa na kungiyar ma'aikata ta Ver.di ya nuna adawarsa a gameda mika al'amuran samartd a ruwan sha gaba daya a hannun kamfanoni masus zaman kansu, inda yayi misali da birnin Berlin. A can din, a karshen shekaru na 90, wani bangare na samar da ruwa an mika shi a hannun kamfanoni masu zaman kansu. Yace tun daga wannan lokaci farashin ruwan da jama'a ke amfani dashi a fanfunan su yake tashi, abin da a yanzu ya kai karin kashi 30 cikin dari.

Kuskure mafi muni a game da mika batun samar da ruwa ga jama'a a hannun yan kasuwa masu zaman kansu, kamar yadda yar majalisar Turai ta jam'iyar SPD ta nan Jamus, Evelyn Gebhardt, shine abin da ya faru abirnin London. A can din fiye da kashi 90 cikin dari na albarkatun ruwa yana kwarara ne zuwa karkjashin kasa, saboda kamfanoni masu zaman kansu da aka mika masu alhakin samar da ruwan sun kasa shimfida fanfunan da ake bukata domin daukar ruwa zuwa inda ake bukatarsa. Saboda haka tace.

Resettling Sudanese Returnees
Hoto: UN Photo/Fred Noy

Idan har maida wani al'amari a hannun yan kasuwa masu zaman kansu, hakan yakan haifar da takara. Idan kuma har za'a kawo wani tsari na daidaita batun samar da ruwan, yadda zai zama bai-daya a Turai, to kuwa ana bukatar wani mataki na tabbatar da kare daraja da tsabtan ruwan da za'a rika baiwa jama'a. A tabbatarda cewar ma'aikatan dake aiki a fannin na samar da ruwa basu zauna cikin tsoron makomar wurarensu na aiki ba, kuma ruwan nan ya kasance mai tsabta, an kuma baiwa jama'a shi bisa farashi madaidaici. Hakan kuwa ba zai yiwu ba sai idan an shimfida sharudda da dokokin da suka dace.

Masani kan al'amuran ruwa, Mathias Ladstätter yace shirin hukumar kungiyar hadin kan Turai na kirkiro tsari bai daya a fannin samar da ruwa zai kara zama mummunan al'amari, saboda gundumomi da kanaan hukumomin a mafi yawan nahiyar Turai tuni sun kmika sauran fannoni na rayuwar jama'a, kamar hanyoyin suhuri da samar da karfin lantarki ga hannun kamfanoni ko yan kasuwa masu zaman kansu. (Akwai sauti daga ƙasa).

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita : Zainab Mohammed Abubakar