Brexit: Kulla yarjejeniyar kasuwanci da EU | Labarai | DW | 24.12.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Brexit: Kulla yarjejeniyar kasuwanci da EU

Kungiyar Tarayyar Turai ta cimma matsaya da Birtaniya kan batun kasuwanci watanni 10 bayan da bangarorin biyu suka kasa cimma matsaya kan yadda huldar cinikayya za ta kasance.

Shugabar hukumar zartarwar Kungiyar Taryyar Turai Ursula von der Leyen ta ce sun cimma kyakyawar yarjejeniya kasuwanci madaidaiciya a tsakaninsu, duk da yake sun fuskanci tarnaki kan batun ruwa da kamun kifi a tsawon watannin da suka shafe suna tattaunawa.

Shugabar kungiyar ta ce bangarorin biyu za su ci gaba da tattaunawa kan wasu muhimman batutwa da suka hada da kare muhalli, makamashi da sufuri da kuma tsaro.

Sai dai a na shi bangare Firaminstan Biratniya Boris Johnson, ya ce Birtaniya za ta kasance babbar aminiyar Kungiyar Tarayyar Turai.

"Ya ce na gayawa abokaninmu na EU da cewar ina fata wannan yarjejeniyar za ta kasance wata kafa ta tabbatar da sabon babi a tsakaninmu, sabanin yadda ta kasance mai wahala har na tsawon rabin karni a baya kuma mai cike da farin cikin cimma wannan yarjejeniyar da za ta bamu damar ficewa a cikin sauki 31 gwannan wata".