Bradley Manning ya nemi ahuwar kotun Amirka
August 15, 2013Talla
Bradley Manning wanda ke magana a gaban wata kotun soji wadda nan gaba kaɗan za ta bayyana hukucin da ta yanke masa, ya kasance cikin ɓacin rai a gaban babbar alƙalin kotun Denis Lind inda ya nemi ahuwa.
Ya dai tabbatar da cewar ya miƙa bayanai na siri na soji da na diflomasiya har dubu 700 ga shafin, sai dai ya musunta cewar ya yi haka ne da nufin cutawa Amirka. Kuma zai iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekaru 90 a kan tuhumar da ake yi masa.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu