1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bouteflika ya sanar da ajiye takarar sa a zaben 17 ga watan Afrilu.

March 4, 2014

A wata bayyana da yayi ta gidan Talbijin na kasar, Shugaban kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika ya sa hannu kan takardar tsayawar sa takara a karo na 4.

https://p.dw.com/p/1BIxp
Hoto: DW/T. Bougaada

A yammacin wannan Litinin din (03.03.2014) ne dai Talbijin din kasar ta Aljeriya ta nuna hoton shugaban ya je ofishin tsarin mulkin kasar cike da walwala zaune gaban wani teburi yana sa hannu kan takardar ajiye takarar sa.

Wannan ajiye takardar takarar ta Shugaba Bouteflika dai ta kawo karshen jita-jitar da ake yadawa, na yiwuwar tsayawa tasa takarar a karo na hudu.

Sai dai a cewar 'yan adawar kasar, shugaban dan shekaru 77 da haihuwa ba shi da cikakkiyar lafiyar cika ayukansa, na wani sabon shugabancin kasa tun bayan kwantar da shi da akayi na tsawon lokaci a birnin Paris na kasar Faransa.

Amma kuma duk da rashin karfin jikin da yake da shi, Bouteflika na cike da tabbacin cewa zai sake cin zaben na ran 17 ga watan na Afrilu, tare da goyon bayan Jam'iyar sa ta Frond de Liberation National da ke jagorancin kasar tare da sojojin kasar tun bayan samun mulkin kan kasar a shekarar 1962.

Tuni dai hadin gwiwar 'yan adawar kasar suka yi kira da a kauracewa wannan zabe.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Saleh Umar Saleh