1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyya mai mulki ta lashe zaben shugaban kasa

Ramatu Garba Baba
October 25, 2019

Jam'iyyar BDP  mai mulki a kasar Botswana ta kayar da jam'iyyar hadaka ta UDC bayan da ta lashe babban zaben shugaban kasa dana 'yan majalisu da ya gudana a ranar Larabar da ta gabata.

https://p.dw.com/p/3Ru7c
Botsuana Parlamentswahlen Mokgoweetsi E.K Masisi
Hoto: Getty Images/AFP/M. Bhuiyan

Jam'iyyar ta lashe kujeru 29 na 'yan majalisar dokoki bayan da ta samu kashi 51 cikin dari na kuri'un da aka kada.Wannan na nufin nasarar ga Shugaba Mokgweetsi Masisi kamar yadda alkalin alakaln kasar ya sanar, har yanzu ana ci gaba da kidayar kuri'un a zaben da shi ne irinsa na farko da kasar ke gudanarwa tun bayan samun 'yanci a shekarar alif da dari tara da sittin da shida.


BDP mai mulki ta fuskanci zazzafar hamayya daga jama'iyyar adawa ta hadaka ta UDC, da ke ikirarin neman sauya fassalin kasar ta fuskar inganta tattalin arzikinta.