1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya: Johnson ya fada rudanin siyasa

Abdoulaye Mamane Amadou
July 7, 2022

A yayin da ake cigaba da samun ministocin gwamnatin Birtaniya da ke marabus, firaministan kasar Boris Johnson ya yi fatali da jingine mulki duk da matsin lamba.

https://p.dw.com/p/4Dmfa
UK Fragen für den Premierministers | Boris Johnson
Hoto: Frank Augstein/AP Photo/picture alliance

Framinista Boris Johnson na kara shiga tsaka mai wuya da rudanin siyasa a Birtaniya bayan da ya ki na'am da yin bankwana da mulki, duk da karaye-kirayen da bangarorin siyasar kasar ke yi masa na cewa ya yi marabus.

Rahotanni sun ce wata tawagar abokan tafiyar Mista Johnson ciki har da kusoshin fadarsa sun bukace shi da ya jefar da kwallon mangwaro ya huta da kuda, bukatar da firaministan ya yi fatali da ita a jiya, yana mai cewa hakan ka iya jefa Birataniya cikin mawuyacin hali da rudani na siyasa.

Ko a wannan Laraba daya daga cikin sabbin ministocin gwamnatin Johnson Simon Hart jim kadan bayan nada shi ya yi marabus, inda ya bi sahun wasu daga cikin ministocin kasar da suka kara kyaure daga gwamnatin, kana suke ci gaba da nuna bukatar da shugaban gwamnatin ya yi marabus.