1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boris Johnson ya sha alwashin yin Brexit a Oktoba

Gazali Abdou Tasawa
July 24, 2019

Sabon firaministan Birtaniya Boris Johnson ya jaddada aniyarsa ta aiwatar da shirin ficewar Birtaniya daga cikin kungiyar tarayyar Turai a ranar 31 ga watan Oktoba mai zuwa ko da yarjejeniya ko babu.

https://p.dw.com/p/3Mg45
UK Boris Johnson hält Rede vor Downing Street
Hoto: Getty Images/J. J. Mitchell

Boris Johnson ya bayyana wannan matsayi nasa ne a jawabin farko da ya gabata jim kadan bayan kaddamar da shi a kan mukaminsa a wannan Laraba a fadar Buckingam a gaban Sarauniya Elizabet ta biyu. Sabon firaministan kasar ta Birtaniya mai shekaru 55 da kuma ya maye gurbin Theresa May a wannan Laraba ya ce ya kamata al'ummar Birtaniya ta kwana da shirin yiwuwar raba garin da Brussels ba tare da yarjejeniya ba.