1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi arangama a Guinea

October 23, 2018

'Yan sandan a Conakry sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla don tarwatsa matasa daga bangaren jam'iyyar adawa wadanda ke yin bore kan sakamakon zabukan kananan hukumomin da ya gudanan tun watan Febrairun bana,

https://p.dw.com/p/3746n
Guinea Wahl Wahlen Unruhen Polizei UFDG Conakry Flash-Galerie
Hoto: AP

'Yan adawan dai sun yi biris da haramta zanga-zangar wanda hukumomi suka yi. 'Yan sanda sun yi kokarin hana daruruwan masu zanga-zangar da suka so datse zirga-zirgar ababen hawa a Conakry babban birnin kasar ta guinea, abin da ya sa matasan suka yi ta jifan 'yan sanda da duwatsu, yayinda su kuwa 'yan sanda suka mai da martani ta cilla wa masu boren hayaki mai sa kwallan. Shugaban rundunar yaki da tarzuma ta 'yan sandan kasar Guinea, General Ansoumane Camara, ya ce sun fito ne don kawar da duk wanda ke son sabawa doka da oda, kuma hana ababen hawa zirga-zirga abu ne da hukuma ba za ta lamunta ba. 'Yan adawa na zargin gwamnati da nada shugabannin kananan hukumomi, duk  bayan da gwamnatin ke kin yin zabe don gwanmnati ta haggi faduwa in zabe mai adalci ya gudana. Don haka ka yi ta daga zaben kananan hukumomi sau da dama. Shugaban 'yan adawan kasar ta Guinea Cellou Dalien Diallo, ya ce 'yan sanda sun harbi motarsa da harsashin gaske inda hakan ya fasa gilashin motarsa, wanda ta kai ga raunata direbansa.