Boren tunawa da hambarar da Morsi a Masar | Labarai | DW | 03.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boren tunawa da hambarar da Morsi a Masar

'Yan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi na niyar tayar da kayar baya sakamakon cika shekara guda da hambarar da shugabansu Mohamed Morsi daga kujerar mulki.

Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta kasar Masar ta nemi magoya bayanta su gudanar da zanga-zanga don numa bacin ransu, albarkacin cika shekara guda da hambarar da shugaba Mohamed Morsi daga karagar mulki da sojoji suka yi. Sai dai kuma hukumomin kasar ta Masar sun jibge sojoji a wuraren da 'yan kungiyar suka saba yin amfani da su don tayar da kayar baya.

Zanga-zangar dai na zama zakaran gwajin dafi ga Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi saboda gwamnatin da ke ci a yanzu ta sanyata a sahun kungiyoyin ta'ada. Wannan kungiya da aka kafata tun shekaru 80 da suka gabata, ita ce ta lashe zabukan da aka gudanar bayan juyin juya halin da ya kawo karshen mulkin Hosni Mubarak. Amma kuma shugabanta Mohamed Morsi da sojoji suka hambarar na iya fuskantar huklunci rai da rai sakamakon tuhumarsa da ake yi da laifuffuka iri daban daban.

A cikin shekara guda an kiyasta cewa fiye da 'yan kungiyar dubu da 400 ne suka hallaka a lokacin wani sumame da sojoji suka kai a wuraren gamgamin 'yan kungiyar ta 'Yan Uwa Musulmi.

Mawallafi: Ramatou Issa Ouanke/MAB

Edita: Usman Shahu Usman