Boren kin jinin gwamnatin Thailand | Labarai | DW | 29.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boren kin jinin gwamnatin Thailand

Mutane sama da dubu sun kutsa kai hedikwatar rundunar sojin Thailand inda suke neman sojin da su hambarar da gwamnatin firaministar kasar Yingluck Shinawatra.

default

Firaministar Thailand Yingluck Shinawatra

Wakilin kamfanin dillancin labarai na Reuters da ya shaida faruwar wannan lamari da ya wakana dazu ya ce mutanen sun yi ta rera kalamai na kin jinin firaminita Shinawatra inda a hannu guda suka nemi jin ta bakin sojin dangane da matsayinsu game da cigaban da kasancewar firaminitar kan gadon mulki.

A sauran sassan babban birnin kasar Bangkok, masu zanga-zanga sun hallara a gaban ofishin jam'iyyar da firaministan kasar ke jagoranta inda suka yi ta nuna adawarsu da cigaba da jagorantar gwamnatin kasar da ta ke yi.

Wannan dai na zuwa ne bayan da firaministar ta tsallake rijiya da baya a wata kuri'a ta yanke kauna da 'yan majalisar dokokin kasar suka kada a jiya.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu