Boren adawa da ta-zarce a Brazzaville | Labarai | DW | 21.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boren adawa da ta-zarce a Brazzaville

A kasar Kongo Brazzaville mutane hudu suka mutu wasu 10 suka jikkata a lokacin da masu zanga-zanga suka fantsam, kan titi don yin adawa da ta-zarcen shugaba Denis Sassou Nguesso.

Tarzumar dai ta barke ne bayan da hukumomin kasar suka fidda sanarwar haramta boren da aka shirya gudanarwa ranar Lahdi mai zuwa, don yin adawa ga kwaskwarimar kundin tsarin mulkin kasar, don bude kofa ga ta-zarcen shugaba Sassou Nguesso. Bisa yunkurin da ya ke yi na zama da daga cikin shugabannin sai mutu ka raba da mulki, shugaba Nguesso in ya samu murde kundin tsarin mulkin to zai kasance kan mulki na shekaru 30. An dai tsare mutane da yawa a Brazzaville babban birnin kasar.