Boren adawa da soji a Masar | Labarai | DW | 03.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boren adawa da soji a Masar

Magoya bayan hambararren shugaban Masar na ci gaba da boren neman a dawo da gwamnatin farar hula.

Dubun dubatan magoya bayan hambararren shugaban Masar Mohammed Mursi, sun sake yin jerin gwano a kan titunan birnin alQahira, fadar gwamnatin kasar cikin dare, inda suke ci gaba da neman a dawo da zababbiyar gwamnatin dimokradiyya a karkashin jagorancin Mursi. Dama fiye da wata guda kenan, magoya bayan Mursi suka fara yin zaman dirshan, inda suke neman a mayar da shi a gadon mulki. Kafofin yada labaran gwamnatin kasar ta Masar sun ruwaito cewar, jami'an tsaro za su kawar da masu boren daga wasu wurare biyu, da ke birnin alQahira, inda suka kafa sansaninsu tun a ranar uku ga watan Yuli.

A halin da ake ciki kuma, Kungiyar 'Yan uwa Musulmi ta yi Allah wadai da wasu kalaman da sakataren kula da harkokin wajen Amirka John Kerry ya yi a wannan Jumma'ar 803.08.13), inda ya nuna alamar goyon bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar ta Masar, kana ya ambata cewar, akwai fararen hular da ke mulki a kasar, wadanda ke kokarin maido da tsarin dimokradiyya. Sai dai kuma magoya bayan Mursi suka ce babu yanda za a yi sojoji su kare tafarkin dimokradiyya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar