Boren adawa da gwamnatin Yukren | Labarai | DW | 23.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boren adawa da gwamnatin Yukren

'Yan adawa a Yukren na ci gaba da fafutukar neman shugaban kasar ya yi murabus.

'Yan adawa a kasar Yukren, sun sha alwashin ci gaba da gudanar da boren neman kasarsu ta karkata ga Kungiyar Tarayyar Turai wajen kyautata huldar kasuwanci. Suka ce ba za su gajiya ba ko da kuwa a yayin hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara ne. Kimanin masu bore dubu 100 ne suka yi gangami a dandalin samun 'yanci dake Kiev, babban birnin kasar a wannan Lahadin (22. 12. 13), yini na biyar kenan - a jere, bayan da shugaba Viktor Yanukovich ya janye daga batun kulla yarjejeniyar kasuwanci tare da Kungiyar Tarayyar Turai. A dai ranar Talatar (17. 12. 13) da ta gabata ce, Rasha ta sanya hannu akan yarjejeniya tare da Ukrain, wadda ta tanadi rage farashin iskar gas da Yukren ke saya daga hannunta da kimanin kaso daya cikin uku, kana Rashar kuma ta sayi takardun lamuni daga Yukren na kimanin kudi dalar Amirka miliyan dubu 15. Har yanzu dai, masu boren, na neman gwamnati ta yi murabus, tare da kiran gudanar da zabukan shugaban kasa gabannin w'adin da kasar ta tsara yi tunda farko.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal