Boren adawa da gwamnati a Yukren | Labarai | DW | 01.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boren adawa da gwamnati a Yukren

A ɓurinsu na samun sauyin gwamnati, 'yan adawa a Yukren sun buƙaci gudanar da sabbin zaɓuka a ƙasar.

'Yan adawa a ƙasar Yukren suna yin kira a gudanar da zaɓuka a ƙasar gabannin lokacin da aka tsara yin hakan. 'Yan adawar sun gabatar da wannan buƙatar ce bayan da 'yan sandan kwantar da tarzoma sun kutsa cikin masu gangamin goyon bayan Ƙungiyar Tarayyar Turai a ranar Asabar (30. 11. 13). Mutane da dama ne suka sami raunika yayin da jami'an 'yan sandan suka farma masu zanga-zangar nuna adawa da matakin da shugaban ƙasar Viktor Yanukovych ya ɗauka, na ƙin sanya hannu a kan yarjejeniyar ƙulla hulɗa da Ƙungiyar Tarayyar Turai.

'Yan sandan sun fito ne ƙwansu da kwarkwatansu bayan da dubbannin masu zanga- zanga suka hallara a Kiev, babban birnin ƙasar, domin neman shugaba Viktor Yanukovych yayi murabus. Ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi matuƙar Allah wadai da tsattsauran matakin da jami'an 'yan sandan suka ɗauka wajen mayar da martani ga masu boren, inda ƙungiyar ta bukaci hukumomin ƙasar su gudanar da bincike dangane da hakan.Manyan jam'iyyun adawar ƙasar guda uku sun haɗa gwiwa wajen yin kira ga yajin aikin gama gari a ƙasar domin tilasta wa shugaba Viktor Yanukovych yin murabus.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Abdurahamane Hassane