1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Bolibiya na murnar murabus din Morales

Zainab Mohammed Abubakar GAT
November 11, 2019

Al'ummar Bolibiya ta fantsama a saman manyan biranen kasar domin nuna farin ciki bayan murabus din Shugaba Evo Morales daga kan mulki a bisa matsin lamba na 'yan kasa.

https://p.dw.com/p/3SprG
Nach der Wahl in Bolivien
Hoto: picture-alliance/dpa/G. Brito

Babban birnin kasar Bolibiya watau La Paz ya kwana cikin tashe-tashen hankula da suka kai ga kone gine-gine, da ke zama martani biyo bayan murabus din Evo Morales, wanda ke shugabantar kasar tun daga shekara ta 2006, sakamakon matsin lamba kan zaben watan da ya gabata. 


'Yan kasar ta Bolibiya dai sun kwana dare suna bukukuwan murna a birnin La Paz bayan samun labarin sauyin mulkin shugabancin kasar. Bayan tsawon shekaru 14 yana kan kujerar shugabanci, inda yake fuskantar karuwar adawa matsananciya,  Evo Morales ya yar da mongoro domin ya huta da kuda a wata sanarwar da ya yi ta gidan talabijin na kasa:

"Na yi murabus daga shugabancin kasa. Dalilin da na yi murabus? Saboda shugabannin adawa Carlos Mesa da Luis Fernando Camacho su daina damun 'yan uwana, kana su kyale bibiyar kungiyoyi. Domin su daina kone-konen gidajen gwamna da na 'yan majalisa da jami'an zartarwa. Kuma su daina sace-sacen mutane suna garkuwa da su".

Murabus din Morales dai ya ya biyo bayan tashin hankalin sa'o'i 24, inda sannu a hankali al'ummar kasar ta bijire masa. Jami'an 'yan sanda sun kaurace wa wuwaren aikinsu domin hadewa a gangamin adawa da shi.  Nan take sai sanarwa ta fito daga kwamandan rundunar sojin kasar Williams Kaliman da ke kira ga shugaban da ya sauka daga mulki don kawo zaman lafiya:

Bolivien Präsident Evo Morales kündigt Neuwahlen an
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Karita

" Rundunar dojin Bolibiya na sanar da al'umma cewar, saboda karuwar tashe-tashen hankula da kasar ke kara tsunduma ciki, wanda ke barazana ga rayukan mutane, babu alamun gwamnatin mulkin farar hula za ta iya shawo kan matsalar bisa la'akari da tanadin sashi na 20 na dokar soji. Don haka muke kira ga shugaban kasa da ya yi murabus daga kujerar mulki, domin zaman lafiyar al'ummar Bolibiya".

Bolibiya dai ta tsinci kanta cikin yanayin wadi na tsaka mai wuya cikin makonnin da suka gabata, wanda sannu a hankali ya jagoranci manyan jami'an gwamnati kama daga mataimakin shugaban kasa da manyan makarrabansa, suka janye daga mulkin kasar. 

A birnin Santa Cruz da ke yankin gabashin kasar, mutane sun yi cincirindo ana ta bukukuwa dangane da murabus din Shugaba Morales. Sai dai fitaccen dan adawa a yankin mai suna Waldo Albarracin ya sanar ta shafinsa na twitter cewar an kone gidanshi.

Bolivien Evo Morales auf der Titelseite einer Zeitschrift
Hoto: picture-alliance/dpa/EPA/M. Alipaz

Duk da cewar Shugaba Morales ya yi murabus, shugabannin 'yan adawa na ganin cewar har yanzu da sauran tafiya a fafutukar da suke ta cimma gaci. Luis Fernando Camacho shi ne jagoran 'yan adawa a Bolibiya:

" Har yanzu muna da Nicaragua kazalika Cuba. Bolibiya za ta zame babbar fata mai abin koyi ga sauran kasashen yankin Latin Amurka, domin korar tsarin mulkin kwaminisanci tare da samar da tsarin mulkin dimukuradiyya da walwala a yankin baki daya. Mu al'ummar Bolibiya za mu jagoranci fafutuka a Venezuela domin maido da martabarta, kamar sauran kasashen duniya da aka ci zarafinsu".

Da farko dai babu masaniya dangane da wanda zai ja akalar kasar, kafin a gudanar da sabon zabe, duk da cewar dan majalisar dottijai na jam'iyyar adawa Jeanine Anez, ta sanar da cewar za ta dauki nauyin hakan.

A karkashin tsarin mulkin Bolibiya dai, idan kasar ta tsinci kanta a yanayi na rashin shugaban kasa da mataimakinsa, shugaban majlisar dottijai ne ya kamata ya karbi akalar mulki. Sai dai a jiya Lahadin shi ma shugaban majalisar Adriana Salvatierra ya yi murabus.