Boko Haram ta yi ikirarin sace Faransawa | Labarai | DW | 26.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta yi ikirarin sace Faransawa

Kungiyar Boko haram ta bukaci a sako 'yayanta da ke tsare a kasashen Kamaru da Najeriya matikar ana so ta sallami Faransawa bakwai ciki har da yara kanana da ta ke garkuwa da su.

Kasar Faransa ta bayyana cewa kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin sace wasu 'yan kasarta bakwai a makon da ya gabata a arewacin Kamaru. Ministan harkokin wajen wannan kasa Laurent Fabius ya fitar da wata sanarwa tun a ranar litinin, inda ya nunar da cewa kungiyar ta watsa wani faifai na bidiyo a shafin You Tube inda ta ce ita ce ke garkuwa da su.

Uku daga cikin 'yayan na kungiyar Boko Haram ba su rufe fuskokinsu ba lokacin da suke bayani, inda daya daga cikinsu ya yi kira da a sako 'yan uwansu da ke tsare a Kamaru da Najeriya, matikar ana so su sallami mutanen da suke garkuwa da su. Su dai wadannan faransan bakwai cki kuwa har da yara kanana, an sace su ne lokacin da suke yawan bude ido a wuraren shakatawa na Waza da ke kusa da Tarayyar Najeriya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu