Boko Haram ta ce ba ta tsaigaita wuta ba
July 13, 2013Talla
Ƙungiyar ta ce ta goyi bayan harin da aka kai a wata makaranta da ke a garin Mamudo a jihar Yobe wanda ke a yankin arewa maso gashin ƙasar, amma kuma ba tare da ɗaukar alhakin kai harin ba.
A cikin wani sabon sako na faifayin Bidiyo da ƙungiyar ta fitar, ta ce ba ta kai hari a kan 'yan makaranta. Yan makaranta kusan 42 suka mutu a harin da aka kai da makamai a farkon wannan wata a garin na Mamudo akan wata makaratar ta Sakandri.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh