1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta ce ba hannun ta a sace turawan Birtaniya da Italiya

Usman ShehuMarch 10, 2012

Ƙunigiyar Boko Haram ta ƙaryata iƙirarin da shugaba Goodluck Jonathan ya yi kan sace turawa, inda ƙungiyar tace sam babu hannun ta a sace Turawan da aka yi a Sokoto

https://p.dw.com/p/14Ica
Nigeria/Kriminalität/Terrorismus Schlagworte: Sokoto, Nigeria, Kidnapper, Geiseln, Terror, Boko Haram Wer hat das Bild gemacht?: Aminu Abdullahi Abubakar (DW Korrespondent) Wann wurde das Bild gemacht?: 09.03.2012 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Sokoto / Nigeria Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? Bild 1: Haus in dem Radikalislamisten in Sokoto Nigeria zwei europäsche Geiseln getötet haben.
Gidan da aka yi gumurzun ƙwato Turawan da aka sace a SokotoHoto: DW/A.Abubakar

Ƙungiyar Boko Haram ta musanta cewa membobin ta ne suka kama turawan da aka yi garkuwa dasu na tsawon watanni goma waɗanda aka kashe a yunƙurin ceto su a Sokoto. A wani labarin da wakilinmu Al'Amin Muhammed ya aiko mana, yace Kakakin kungiyar Abul Qaqa ya shaida qa manema labarai cewa ba su taba kame wani suyi garkuwa da shi don nemna kudi ba, wannan ba tsarin su bane, su suna da hanyar da suke bi na daukar fansa ko aiwatar da gargadin su ga wanda suke fada shi. Abul Ƙaƙa Ya kuma garhadi wasu kafafen yada labarai da su guji nuwa banbanci ko son zuciya wajen yada bayanai kan abinda ya shafe ƙungiyar, in ba haka ba za su gamu da fushin kungiyar. Kungiyar Boko Haram ta kuma dauki alhakin hallaka jami'n Kwastam din nan a garin Potiskum tare da hare-haren da aka kai a Ashaka da Gaidam da Konduga, dukkanin su a yankin Arewa maso gabashin Najeriya. A wani labarin kuma wasu ‘yan bindiga sun hallaka wani babban Jami'in ‘Yan sanda mai jagorancin rundunar yaki da ta'addanci ta jihar Adamawa mai suna Muhammad Ali a kan hanyar Atiku Abubakar dake Jimeta dake kusa da Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa. Haka kuma da daren jiya wasu ‘yan bindigar sun harbe Alhaji Bello Kagarawal dagacin Annguwar Kagarawal dake Gombe.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Abdullahi Tanko Bala