Boko Haram ta ƙwace wata cibiyar ′yan sanda a Gwoza | Labarai | DW | 21.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram ta ƙwace wata cibiyar 'yan sanda a Gwoza

Rahotanni daga jihar Borno ta Najeriya na nuna cewar wasu ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan Ƙungiyar Boko haram ne sun karɓe iko da wani kwalejin horar da ‘yan sanda da ke garin Limankara a ƙaramar hukumar Gwoza.

Wasu da suka shaida abin da ya faru sun bayyana cewar da misalin ƙarfe uku na safe ne ‘yan bindigar suka afkawa wannan kwaleji, Wanda ke horar da ‘yan sanda kuma suka karɓi iko da ɗaukacin wurin.

Akwai kuma wasu rahotannin da ke cewar garin Buni Yadi na jihar Yobe shi ma ya faɗa hannun ‘yan ƙungiyar inda suka kafa tutocinsu da kuma fara aiwatar da mulkin garin bisa tsarinsu. Ya zuwa yanzu jami'an tsaro ko gwamnatin Najeriya ba su ce komai ba kan hare-haren da suka yi sandiyyar ƙwace wannan makaranta ta horar da ‘yan sanda . Haka kuma babu rahotanni na addadin mutanen da hare-haren suka rutsa da su.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu