Boko haram ta ƙwace garin Buni Yadi | Labarai | DW | 21.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko haram ta ƙwace garin Buni Yadi

Rahotanni daga jihar Yobe da ke a yankin arewa maso gabashin Najeriya na cewar masu fafutuka na Boko Haram sun ƙwace iko da garin Buni Yadi.

wani kakakin gwamnan jihar Yoben Abulahi Gaidam ya shaidawa kamfanin dilanci labarai na Faransa AFP cewar babu wani sojin gwamnati ko ɗaya da ke a can a halin yanzu.

Shaidu waɗanda suka tsere daga garin sun ce mayaƙan na Ƙungiyar Boko Haram sun kafa sansanisu a wani gini gwamnatin inda suka kafa tuttarsu,sannan kuma suka ce 'yan ƙungiyar sun kwashi ganima a cikin shaguna.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe