Blair zai gana da Mr Olmert da Mr Abbas | Labarai | DW | 18.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Blair zai gana da Mr Olmert da Mr Abbas

Faraministan Biritaniya Mr Tony Blair ya isa kasar Israela, aci gaba da ziyarar daya kai yankin Gabas ta tsakiya. A dai wani lokaci ne a nan gaba, Mr Blair zai gana da Faraministan Israela Ehud Olmert da kuma Jagoran palasdinawa Mahmud Abbas.

Kafafen yada labarai dai sun rawaito Blair na cewa babban abin yi a yanzu haka shine, daukar matakan shawo kann rikicin dake faruwa a tsakanin Israela da Palasdinawa.

Ana dai sa ran a lokacin ganawar sa da jagoran palasdinawa, Mr Blair zai nuna goyon bayan sa ga zaben da Mr Mahmud Abbas ya bukaci gudanarwa a yankin.

Kafin dai barin Mr Blair madafun ikon kasar Biritaniya a shekara ta 2007, akwai alamun cewa zai yi iya kokarin sa na ganin an cimma maslaha a tsakanin Israela da Palasdinawa.