Bitar shekara a kan batun siyasa a Najeriya | Siyasa | DW | 31.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bitar shekara a kan batun siyasa a Najeriya

Babban abin da ya fi ɗaukar hankali a wannan shekara ta 2015 da ke shirin kammala, shi ne zuwa Muhammad Buhari kan karagar mulki.

Sabon shugaban Najeriya Muhammad Buhari ke nan ke rantsuwar kamun aiki a ranar 29 ga watan Mayun da ya shuɗe a wani abin da ke zaman ƙoƙari na kafun tarihi na siyasa cikin ƙasar.

Dan shekaru 73 Buharin dai yai nasarar karɓe goruba a hannun kuturu a cikin mulki dama siyasar ƙasar dake nuna alamun rikiɗewa ya zuwa tsarin mai ƙarfi sai Allah.

Nasara Buhari a zaben Najeriyar wani babban misali ne a Afirka

Zaɓen na shekara ta 2015 ne dama yaƙin neman zaɓen da ya kai ga gabatarsa sannan kuma da rawa ta masu siyasar da ke ƙara baiyyana a halin yanzu ke zaman muhimmai na batutuwa na siyasar da suka ɗauki hankali na 'yan kasar a sekarar mai ƙarewa.Duk da cewar dai Buharin yai nasarar cira tuta a zaɓen da ake yi wa kallon mafi tsafta a tarihin jamhuriya ta Huɗu da kuma yai nasarar kare babakeren mulkin PDP na shekau 16, a gaba ɗaya manyan yayan ƙasar ta Najeriya uku ne dai ke takara ta gwarzo a fagen siyasar

Amincewar Goodluck Ebele jonathan cewar ya sha kaye a zaɓen

To sai dai kuma in har nasarar ta Buhari na zaman babu irinta , 'yan ƙasar na kuma kallo ga shi kansa tsohon shugaban kasar Goodluck Ebele jonathan da Buharin ya yi nasarar kayarwa a matsayin wani gwarzon da ya sadaukar da ɓuri dama aládar gado ta shugabanni da nufin yin kaka gida a kan mulkin.