1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin korarminista Musulma a Birtaniya

January 23, 2022

'Yan majalisar dokokin Birtaniya sun yi kira da a kaddamar da bincike bayan da tsohuwar karamar ministar sufuri ta kasar Nusrat Ghani ta yi zargin an cire ta daga mukaminta saboda ita Musulma ce.

https://p.dw.com/p/45yoz
London Nusrat Ghani  MP UK
Hoto: David Cliff/AA/picture alliance

A cikin hirar da ta yi da jaridar Sunday Times ta Birtaniya ne dai, 'yar siyasar ta ce wani jigo a jam'iyyar Conservative ya shaida mata cewa halayenta na Musulumci aka yi nazari a kai kafin tunbuke ta da fadar Downing Street ta yi a shekara ta 2020. Ofishin Firaminista Boris Johnson dai ya ce tuni ya gana da ita, ya kuma ba ta shawarar yadda za ta nemi hakkinta. Ministan lafiya Sajid Javid da ministan ilimi Nadhim Zahawi sun nuna rashin jindadinsu kan lamarin, inda suka lashi takobin yi wa tsohuwar karamar ministar jagora zuwa ofishin da za ta shigar da korafi.