1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin farko zai tashi zuwa Ruwanda daga Birtaniya

Abdourahamane Hassane
June 14, 2022

Nan gaba a yau zuwa da yamma aka shirya jirgin farko na wadanda Birtaniya ta hanawa mafaka zai sauka a birnin Kigali na kasar Ruwanda.

https://p.dw.com/p/4CgzX
Großbritannien Protest gegen die Abschiebung von Geflüchteten zurück nach Ruanda
Hoto: Niklas Halle'n/AFP/ Getty Images

Mutane akalla 30 da Birtaniya ta zarga da shiga kasar ba bisa kaida ba, za a mayar da su Ruwanda a yau, tun farko an dage batun mayar da su Ruwanda a sakamakon karar da wasu kungiyoyi masu rajin kare hakkin bil'Adama suka shigar na kalubalantar matakin mahukuntan Britaniyan amma bayan rashin nasara a gaban kotun daukaka karar aka ci gaba da aiwatar da shirin.Britaniya ta cimma yarjejeniyar dala miliyan 151  da Ruwanda kan karbar mutanen