SiyasaTurai
Za a fara daukar masu HIV aiki a sojojin Birtaniya
December 1, 2021Talla
Kazalika sojojin sun ce daga shekara mai zuwan za su rika tura jami'an sojoji masu HIV/AIDS da shan magani ya taimaka musu rage kaifin cutar a fagen daga.
Hakan na zuwa ne a yayin da a wannan Laraba ake bikin cika shekaru 40 da duniya ta fara yaki da cutar bayan ganowa a karon farko. Kafin sanarwar da Birtaniya ta yi a wannan Laraba, galibin kasashen duniya ciki har da Amirka ba sa daukar masu HIV/AIDS aiki a cikin rundunar soji ko kuma 'yan sanda.
Tuni dai masu dauke da cutar a Birtaniya suka jinjina wa gwamnati kan matakin da suke ganin zai ba su damar da suka jima suna neman samu.