Taron kasuwancin Afirka da Birtaniya
January 20, 2020Talla
Wannan dai shi ne karo na farko da za a gudanar da taron kasuwanci da habaka tattalin arziki tsakanin Birtaniya da kasashen na Afirka.Yayin taron ana sa ran Firaminista Boris Johnson zai bayar da muhimmanci wajen jan hankalin 'yan kasuwa da masu masana'antu a Afirka, su zuba jari a Birtaniya da zarar ta kammala ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai EU.
Daga cikin shugabannin kasashen Afirkan da zasu halarci taron, akwai shugaba Muhammadu Buhari na Tarayyar Najeriya da takwarorinsa na kasashen Masar da Kenya da kuma Ghana.