1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar ficewa daga kungiyar EU ta samu karbuwa a majalisa

Abdoulaye Mamane Amadou
December 20, 2019

Majalisar dokokin Birtaniya ta amince da kudrin dokar ficewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai da Firaminbista Boris Johnson ya shigar a gabanta.

https://p.dw.com/p/3VAHl
Großbritannien London | Erste Parlamentssitzung nach Unterhauswahl
Hoto: picture-alliance/empics/House of Commons

Da gagarumin rinjaye ne dai majalisar dokokin kasar ta Birtaniya ta aminta da sabon kudrin dokar lamarin da tun daga farko masu sharhi ke kallon cewa da hakan za ta kasance duba da gagarumin rinjayen da a zaben 'yan majalisun dokokin da jam'iyyar konservative ta Boris Johnson ta samu gagrumin rinjaye.
Wannan dai na nuni da cewa a yanzu Birtaniya ta yi wani hubbasa a yunkurinta na ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai kan nan zuwa 31 ga watan gobe na sabuwar shekara, kana kuma ana sa ran a ranar 09 ga watan gobe majalisar dokokin kaar ta kada kuri'ar amincewa da yarjejeniyar ficewar kasar baki daya daga EU