1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan majalisar dokokin Birtaniya za su koma bakin aikinsu

Usman Shehu Usman AH
September 24, 2019

Kotun kolin Birtaniya ta yanke hukuncin cewar dakatar da majalisar dokokin da firaministan kasar Boris Johnson ya yi ba ya bisa doka.

https://p.dw.com/p/3Q9ch
Großbritannien |  Supreme Court in London
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Dunham

Yanke hukuncin da kotun kolin ta yi dai ya zo ba zato ba tsammani ko da kuwa ga su 'yan adawa kamar yadda aka ji wasunsu na fada. Baki dayan alkalan kotun sun ba da ra'ayin cewar firaministan matakin da ya dauka ya sabawa doka kuma hakan tarnaki ne ga aikin 'yan majalisar dokoki. Shugabar kotun kolin Birtaniya Brenda Hale ta ce: "Wannan kotun ta yanke hukunci cewar shawarar firaministan ta neman izinin sarauniya ya sabawa doka. Hakan na nufin umarnin da ya kai ga rufe majalisar shi ma ba ya kan doka, kuma yanzu bai da tasiri an kuma warwareshi. Hakan na nufin takardan da aka kawo majalisar dokoki na umartan rufe majalisar tamkar farar takarda ce da ba ta da rubutu, rufe majalisar ya tashi daga aiki ."