Birtaniya: Jam′iyyar Theresa May ta rasa rinjaye | Labarai | DW | 09.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Birtaniya: Jam'iyyar Theresa May ta rasa rinjaye

Sakamakon zaben 'yan majalisar dokoki da ya gudana a Birtaniya na nuni da cewar Jam'iyyar masu ra'ayin rikau ta firaminista Theresa May ta rasa babban rinjayen da take da shi a baya kafin wannan zabe.

Großbritannien Wahlen 2017 – Wahlausgang - Theresa May (Reuters/T. Melville)

Firaministan Birtaniya Theresa May.

Jam'iyyar ta masu ra'ayin rikau na kasar ta Birtaniya ta rasa babban rinjayen da take da shi a baya idan aka kwatanta ta sakamakon na yanzu da yawan 'yan majalisar da take da shi a baya na 330 kafin wannan zabe, yayin da jam'iyyar ma'aikata ta abokin hamayyar ta Jeremy Corbyn ta samu karin kujeru 37 a gaban wanda take da shi a baya. Firaminista May ta jinjina wa kwarya-kwaryar nasarar da suka samu a wannan zabe duk kuwa da cewar ba sakamakon da suka yi fatan samu ba ne

"A dai dai wannan lokaci fiye da duk wani lokaci, Birtaniya na bukatar yanayi na kwanciyar hankali, da kuma shugabanci mai dorewa bayan zaben raba gardamar ficewa daga Tarayyar Turai da ya gudna a bara.

Sai dai da yake magana shugaban jam'iyyar ma'aikata Jeremy Corbyn ya ce yakin neman zaben da ya yi mai cike da armashi, ya sauya tafiyar siyasar kasar zuwa ga abu mafi dacewa, inda ya nuna gamsuwar sa ga sakamakon zaben da ke nuni da cewa sun kawo sauyi a kasar a cewarsa.

Sai jam'iyya ta samu kujeru 326 ne daga cikin kujeru 640 da ake da su a kasar, take iya kafa gwamnati ita ka dai. Sai dai a halin yanzu dai babu jam'iyyar da za ta iya kafa gwamnati ita ka dai ba tare da ta yi kawance da wata jam'iyya ba.