Birtaniya da Bill Gets za su yaki malariya
January 25, 2016Hamshakin attajirin nan Shugaban Kamfanin Microsoft wato Bill Gates da kuma ministan kudin kasar Birtaniya sun ba da sanarwar a wannan Litinin fito da wani sabon shiri na yaki da cutar zazzabin cizon sabro wacce ta kasance cutar mafi kisa a duniya.
Jaridar The Times wacce ta wallafa labarin ta ruwaito minista George Osborne da Bill Gates na cewa kudi miliyan dubu hudu ne na Euro shirin zai lakume a cikin shekaru biyar masu zuwa a fannin bincike dama duk wasu ayyuka da za su taimaka wajen kawar da wannan cuta.
A karkashin shirin dai a tsawon shekaru biyar masu zuwa a ko wace shekara Birtaniya za ta zuba miliyan 660 a yayin da gidauniyar Bill Gets za ba da miliyan 190.
Rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya WHO na shekara ta 2015 ya bayyana cewa mutane miliyan 214 suka kamu da cutar a shekarar ta bara inda daga cikin sama da dubu 438 suka mutu.