1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Birtaniya: Boris Johnson ya yi murabus

Yusuf Bala Nayaya
July 9, 2018

Wannan dai na nuni da cewa Firaminista Theresa May za ta samu kai a halin tsaka mai wuya kan harkokin mulki.

https://p.dw.com/p/315Qh
UK Brexit | Kabinettsitzung - Außenminister Boris Johnson
Hoto: picture-alliance/NurPhoto/A. Pezzali

Sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson ya yi murabus kamar yadda bayanai ke fita daga Downing Street suka nunar. Wannan dai na nuni da cewa Firaminista Theresa May za ta samu kai a halin tsaka mai wuya kan yadda za ta tafiyar da harkokin mulkin kasar ta Birtaniya. Hakan dai na zuwa ne bayan ajiye mukami da mai shiga tsakani kan batun fitar Birtaniya daga Kungiyar EU David Davis ya yi ranar Lahadi.