Birnin Goma ya faɗa cikin hannu yan tawayen M23 | Labarai | DW | 20.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Birnin Goma ya faɗa cikin hannu yan tawayen M23

Jagoran ƙungiyar yan tawayen na M23 na ƙasar Kwango Sultani Makenga ya yi kira ga sojoji da yan sanda da su ba da haɗi kai ga ƙungiyar

Janar Makenga ya baiyana haka ne jum kaɗan bayan garin Goma ya faɗa cikin hannu dakarun yan tawayen.Masu aiko da rahotanin sun ce Makenga tshohon sojin gwamnatin wanda ya yi marabus a cikin wata Mayo da ya gabata domin kafa ƙungiyar M23 ya zagaya cikin birin Gomar tare da rakiyar bradan sa:

Sai dai har yanzu ana cikin ruɗami dangane da sanarwa da wani babban jamin ƙungiyar yan tawayen kanal Viannay ya baiyana,cewar sun karɓe iko da filin saukar jiragen sama. Abinda wani jami'in rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD wato monusco .ya ƙaryata.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman