1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

BioNTech zai fara sayar da maganin waraka na cancer a 2026

Abdourahamane Hassane
March 20, 2024

Kamfanin gwaje-gwaje na magunguna na Jamus BioNTech, wanda ya kirkiro rigakafin cutar Covid-19,ya ce yana da niyyar fara sayar da maganin farko na waraka daga cutar kansa a cikin shekara ta 2026.

https://p.dw.com/p/4dx1A
Hoto: Hendrik Schmidt/dpa/picture alliance

A halin yanzu kamfanin na BioNTech  yana aiki akan magunguna da yawa akan cututtuka dabam-dabam na kansar wadanda suka hada da kansar mafitsara da huhu  da kansar kwakwalwa wanda za a iya samarwa magani.Gabaɗaya, dakin gwaje-gwaje na Biontech na fatan samun izini kusan goma daga cikin waɗannan jiyya nan da shekarar   ta 2030