Bincikien aurar da yarinya ′yar shekaru tara a Australiya | Labarai | DW | 02.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bincikien aurar da yarinya 'yar shekaru tara a Australiya

Kamar yadda wata kididdiga ta kasa da kasa ta nunar kimanin yara 39,000 kasa da shekaru 18 ake aurarwa a kowace rana a duniya. Lamarin da ke nuna danniya da kanan yara ke fiskanta a kasashe masu tasowa.

Gwamnatin kasar Australiya na gudanar da wani bincike na cewa an aurar da wata karamar yarinya 'yar shekaru tara daga birnin Sydney inda aka dauke ta daga kasar ta Ostareliya zuwa yankin gabas ta tsakiya.

Jami'an gwamnatin kasar ne dai suka bayyana haka a ranar Talatan nan.

Sashen kula da binciken lafiyar baki mata a kasar ya bayyana cewa ya samu wasu bayanai kan wannan zargi inda ya kara da cewa batun aurar da kananan yara mata lamari ne da ake ci gaba da samunsa ba tare da ana bada rahotanni ba.

Babbar darakta a wannan sashi Dakta Eman Sharobeem ta ce tuni aka tura jami'an hukumar dan su je gidan su yarinyar dan tattaunawa da iyayenta, inda suka ce yarinyar za ta dawo kasar ta Australiya nan gaba.

Dakta Sharobeem ta fadawa gidan jaridar Sydney Morning Herald cewa "Babban abin fargaba shi ne makomar yarinyar da abinda ka iya samun ta, idan muka bar wannan zargi ya tafi haka bamu bincika ba to matsalarmu ce".

Kamar yadda wata kididdiga ta kasa da kasa ta nunar kimanin yara 39,000 kasa da shekaru 18 ake aurarwa a kowace rana a duniya akasari daga kasashe masu tasowa.

Mawallafi:Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu