Binciken musabbabin hatsarin jirgin saman Ethiopian Airlines | Labarai | DW | 16.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Binciken musabbabin hatsarin jirgin saman Ethiopian Airlines

Masu bincike kan musabbabin faduwar jirgin saman kasar Habasha a karshen makon jiya sun ce za a dauki dogon lokaci ana yi.

Hukumomin kasar Habasha sun tabbatar da cewar binciken da ake game da musabbabin faduwar jirgin saman kasar da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 157 zai dauki lokaci.

A yayin wata ganawa da 'yan jarida a wannan Asabar ministan sufurin kasar Dagmawit Moges ya ce dole ne hukumomin kasa da kasa su yi gagarumin binciken kwa-kwaf kan faduwar jirgin tare da bayyana matakan da suka cancanta.

A ranar Lahadi da ta gabata ne jirgin saman kasar Habasha mallakar kamfanin sufurin jama'a na Ethiopian Airlines ya fadi mintuna shidda bayan tashinsa daga birnin Addis Ababa kan hanyarsa ta zuwa Nairobin Kenya.