Binciken kisan gilla a Afirka ta Kudu | Labarai | DW | 26.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Binciken kisan gilla a Afirka ta Kudu

Kwamitin da gwamnatin Afirka ta Kudu ta kafa domin binciken wata ta'asa da 'yan sandan kasar suka yi wadda ta janyo asarar rayukan mutane ya fitar da rahotonsa.

Yajin aikin ma'aikatan hakar ma'adinai a Afirka ta Kudu

Yajin aikin ma'aikatan hakar ma'adinai a Afirka ta Kudu

A shekara ta 2012 ne dai 'yan sandan kasar Afirka ta Kudun suka kai wani samame a mahakar ma'adinai ta Marikana inda suka bude wuta a kan ma'aikatan kamfanin hakar ma'adinan na platinum mine da ke yajin aiki, inda suka kashe mutane 34. Kwamitin binciken ya bayyana cewa 'yan sandan sun tafka kuskure sakamakon matakin da suka dauka a kan ma'aikatan da bai kamata ba. Da yake bayani kan rahoton hukumar, shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma cewa ya yi:

"Kwamitin ya gano cewa matakin da 'yan sandan suka dauka a ranan 16 ga watan Agusta na 2012 bai kamata ba. Kwamitin ya kuma gano cewa ba za a iya kwace makamai daga hannun masu zanga-zangar da kuma kawo karshen yajin aikin ba tare da an zubar da jini ba."

Kwamitin dai ya wanke dukkan manyan jami'an gwamnatin kasar daga zargin hannu a kisan gillar da aka yi wa ma'aikatan kamfanin hakar ma'adinan.