Binciken duniya kan ta′asar birnin Bangui | Labarai | DW | 11.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Binciken duniya kan ta'asar birnin Bangui

kwamitin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kare hakkin bil-Adama zai fara bincike kan ta'asar da bangarori biyu da ke gaba da juna suka aikata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Kwamitin da Majalisar Dinkin Duniya ta baiwa izinin wannan bincike da ke a karkashin jagorancin masanin harkokin shari'a dan kasar Kamaru Bernard Acho Muna, zai yi kokarin gano masu hannu a cikin wannan lamari domin su fuskanci shari'a. Kusan shekara guda ke nan da wannan kasa ta shiga cikin wani hali na kashe-kashe tsakanin Musulmi da Kiristoci.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai kasa ce da ke fuskantar ficewar al'ummarta Musulmi ya zuwa wasu kasashen sakamakon dumbun matsalolin da suke fuskanta, inda daga kashi 15 cikin dari na yawan Musulmin wannan kasar, aka dawo a kalla kashi biyu cikin dari a halin yanzu, a cewar mai bada shawara na musamman ga Sakataran MDD, dan kasar Senegal Adama Dieng.

Dakarun sa kai da aka fi sani da suna Anti-Balaka, na ci-gaba da cin karensu ba tare da babbaka ba a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya duk kuwa da sojojin kiyaye zaman lafiyar da ake da su a wannan kasa, inda suke kashe takwarorinsu musulmi, suna kuma kokkonasu tare da cin namansu a wani mataki na ramuwar gayya.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe